Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya amince a mayar da cibiyar raya karkara ta Rano zuwa babbar makarantar koyon fasaha ta gwamnatin tarayya (Federal Polytechnic of Technology) tare da daga darajar babban asibitin Rano zuwa cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin tarayya (Federal Medical Centre).
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron bayyana goyon baya da masu ruwa da tsaki daga Kano ta Kudu suka shirya a garin Rano, domin ayyana Sanata Kawu Sumaila a matsayin ɗan takarar bai ɗaya na jam’iyyar APC.
Gwamna Abba ya kuma tabbatarwa da al’ummar yankin da na jihar Kano cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan ci gaba da more rayuwa domin inganta rayuwar jama’a da sanya jihar a matakin da zata yi gogayya da manyan birane a duniya.
A nasa jawabin, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, ya tabbatarwa gwamnan cikakken goyon bayan al’ummar yankin Kano ta Kudu a zabe mai zuwa domin samun nasara, wanda hakan zai kara baiwa gwamna Abba da Shugaban kasa Bola Tinubu damar ci gaba da aiwatar da managartan ayyuka.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na jaddada cewa salon gwamnatinsa ya sha banban da sauran wadanda suka gabata la’akari da yadda yake sauya fasali da bunkasa kowane fanni a kano domin sanya jihar a matakin da zata yi gogayya da manyan biranen duniya.
