Mataimakin Gwamnan Kano Murtala Sule Garo, ya yabawa Hukumar Hisbah ta jihar bisa kokarin da take yi wajen tabbatar da tarbiyya da yaki da ayyukan rashin da’a a fadin jihar.
Garo ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin shugabannin hukumar Hisbah a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a ofishinsa.
Garo ya kuma yabawa hukumar bisa irin goyon baya da kaunar da take nunawa wajen ci gaban jihar Kano, tare da tabbatar musu da cewa zasu tattauna da Gwamna Abba Kabir Yusuf domin duba bukatun da hukumar ta gabatar.
Tun da farko, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya tunatar da gwamnati wasu daga cikin bukatun hukumar da suka hada da kafa makarantar horas da jami’an Hisbah, karin albashi, sauya kayan aiki, gina sabowar shalkwatar hukumar, samar da karin motocin aiki da kuma kara kudaden gudanarwa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito shugaban Hukumar Hisbah ta Kano, Shehi Shehi Mai Hula, yana taya mataimakin gwamnan murna kan sabon mukaminsa tare da bayyana cewa an dora mutum nagari a gurbin da ya dace.
