Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce kotuna ne za su yanke hukunci na ƙarshe kan cancantar ’yan takarar da aka cire sunayensu daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi na 2027.
Hukumar ta kuma bai wa jam’iyyun siyasa da ’yan takarar da abin ya shafa wa’adin kwanaki 14 domin shigar da ƙorafe-ƙorafe a gaban kotu, idan suna ganin an tauye musu haƙƙinsu.
Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Mohammed Haruna ne ya bayyana hakan.
A cewarsa, hukuncin Kotun Ƙoli ya wajabtawa jam’iyyun siyasa gabatar da rajistar mambobinsu ga hukumar, wadda za ta ƙunshi sunayen mutanen da suka zaɓa domin tsayawa takara a zaɓukan da ke tafe.
Idan ba a manta ba dai dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC Aminu Abdussalam Gwarzo da dan Takarar gwamnan Gombe a jam’iyyar PDP Farfesa Isah Ali Pantami na daga cikin jerin sunayen yan takarar gwamnan da ba a gan su a jadawalin da INEC din ta fitar ba.
