Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya, FAAN, ta karyata rade-radin da ake yaɗawa cewa an sayar da wani ɓangare na filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Jami’ar Yaɗa Labarai ta hukumar, Bilkisu Baffa Usman, ta bayyana cewa zargin da ake yaɗawa kan sayar da wani ɓangare na filin jirgin ba shi da tushe.
Ta ce abin da ake gani a yanzu a filin jirgin shi ne aikin gyaran titunan cikin filin, wanda kamfanin J.R.B Construction Company Nig. Ltd. ke gudanarwa.
Bilkisu Baffa Usman ta ƙara da cewa da zarar an kammala aikin, hukumar za ta sanar da jama’a tare da gayyatar manema labarai domin su je su ga ayyukan da aka gudanar.
A baya-bayan nan, an fara wasu manyan ayyukan inganta ababen more rayuwa a filin jirgin Malam Aminu Kano, ciki har da aikin gyaran titunan saukar jiragen sama, yayin da gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira biliyan 46 domin sake gina wasu muhimman sassan filin jirgin.
