Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilan da suka sa ya ajiye burinsa na zama shugaban Najeriya domin marawa Peter Obi baya a zaɓen 2027.
Kwankwaso ya ce ya ɗauki matakin ne saboda amincewarsa da gaskiya da riƙon amanar Peter Obi, da kuma ganin dacewar ci gaba da bai wa yankin Kudancin Najeriya damar shugabancin ƙasar.
Da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Kano ranar Lahadi, jagoran Kwankwasiyya ya bayyana cewa ya kamata ƴan Najeriya su bai wa Obi damar jagorantar ƙasar domin tabbatar da adalci a tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu.
Kwankwaso, wanda ya ce ya nemi takarar shugaban ƙasa sau uku a jere, ya bayyana cewa ya zaɓi dakatar da burinsa na neman kujerar domin marawa ɗan takarar da ya fito daga Kudancin Najeriya baya.
Ya jaddada cewa shawarar tasa na da nasaba da burinsa na ganin an samu daidaito da adalci a siyasar Najeriya, tare da bai wa Peter Obi damar jagorantar ƙasar.
