Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiTsohon sakataren ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Dakta Muhammad Bello Al-Adam, ya rasu...

Tsohon sakataren ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Dakta Muhammad Bello Al-Adam, ya rasu ranar Asabar a kasar Indiya bayan gajeruwar rashin lafiya.

Date:

Tsohon sakataren ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Dakta Muhammad Bello Al-Adam, ya rasu ranar Asabar a kasar Indiya bayan gajeruwar rashin lafiya.
Da suke sanar da rasuwarsa, iyalan marigayin sun ce za a sanar da shirye-shiryen jana’izar bayan isawar gawarsa nan gida Najeriya.
Al-Adam wanda ya ke dan asalin jihar Kano, ya yi koyarwa a Makarantar Shari’a ta Kano ta Shahuchi,gabannin fara huldar diflomasiyya a ma’aikatar harkokin waje tsakanin shekarar 1984 zuwa 1985.
Al-Adam ya kasance dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin rusasshiyar jam’iyyar UNCP a shekarar 1998.
Ya kuma kasance mamba a jam’iyyun APP, ANPP, CPC da kuma jam’iyyar APC mai mulki inda ya kasance memba a cikin masu ruwa da tsaki na kungiyar yakin neman zaben Tinubu da Shettima na shugaban kasa a zaben 2023.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...