Murabus ɗin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugaban hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa NAHCON, bai zo wa mutane da yawa da mamaki ba, duba da irin rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye shugabancinsa tun bayan hawansa kan kujerar.
Sai dai lamarin ya janyo sabbin tambayoyi kan makomar hukumar da kuma shirye-shiryen aikin Hajjin 2026.
Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ahmed Mu’azu, ne dai ya tabbatar da murabus ɗin a daren Litinin, sai dai ba a bayyana takamaiman dalilin da ya sa ya ajiye mukamin ba a hukumance.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa Farfesa Abdallah Pakistan a shekarar 2024 domin maye gurbin Jalal Arabi, wanda aka cire daga mukaminsa yayin da ake bincikensa kan zargin almundahanar kuɗaɗen Hajjin 2024.
A shekarar 2025, Farfesa Pakistan ya jagoranci gudanar da aikin Hajji karo na farko a matsayin shugaban NAHCON, aikin da ya kasance cike da cece-kuce a hukumar.
Tun bayan hawansa kan muƙamin, an riƙa zargin sa da matsaloli da suka haɗa da rashin kwarewa a wasu fannoni na gudanarwa, zargin fifita wasu a cikin nada mukamai da kuma gazawa wajen tafiyar da muhimman al’amuran da suka shafi aikin Hajji.
Rahotanni sun ce waɗannan zarge-zarge ne suka haifar da saɓani mai tsanani tsakanin sa da wasu mambobin kwamitin gudanarwar hukumar.
A watan Janairun 2026 ne rikicin ya ƙara tsananta, bayan da aka rawaito cewa dukkan mambobin kwamitin NAHCON sun haɗa kai wajen rubuta takardar koke zuwa ga Shugaban Kasa, inda suka nuna rashin amincewa da shugabancinsa.
Takardar ta kunshi zarge-zargen gazawa a shugabanci da kuma salon tafiyar da aiki da ba su gamsu da shi ba.
Majiyoyi sun kuma bayyana cewa Shugaban Kasa bai ji daɗin rahoton rage yawan kujerun Hajji da aka bai wa Najeriya daga dubu 95 zuwa dubu 50 ba, lamarin da aka ce ya shafi dubban maniyyata a fadin kasar nan.
Haka kuma, ana zargin cewa wasu rahotanni daga hukumomin tsaro da kuma binciken kuɗi da Hukumar EFCC ke yi sun ƙara dagula al’amura tare da raunana matsayinsa.
Lamarin ya kai ga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya shiga tsakani, inda ya jagoranci taro da masu ruwa da tsaki domin duba koken da aka gabatar da kuma nemo mafita.
An ce Shugaban Kasa ya ba Mataimakin nasa umarnin yin nazari kan rahotannin da aka gabatar tare da bayar da shawarwari, ciki har da nemo wanda ya fi dacewa ya jagoranci hukumar domin tabbatar da tafiyar da aikin Hajji cikin nasara.
Yanzu haka murabus ɗin Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya buɗe sabon babi a tarihin NAHCON, inda masu lura da al’amuran Hajji ke ganin cewa wannan mataki na iya zama wata dama ta gwada ƙwarewar wasu wajen jan ragamar hukumar, gabanin shirye-shiryen Hajjin 2026.
Ana sa ran gwamnatin tarayya za ta sanar da sabon shugaban NAHCON nan ba da jimawa ba, domin tabbatar da cewa shirye-shiryen aikin Hajji na gaba sun tafi yadda ya kamata, tare da kauce wa duk wata tangarda da ka iya janyo cikas ga maniyyatan Najeriya.
