Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓensa a Jihar Kano a ranar 17 ga Disamba, 2026, bisa jadawalin da jam’iyyar APC ta fitar gabanin babban zaɓen 2027.
Jadawalin ya nuna cewa Kano na daga cikin jihohin da shugaban zai ziyarta a wani ɓangare na gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki.
Kafin zuwa Kano, ana sa ran Tinubu zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓe a Jihar Sokoto a ranar 5 ga Disamba, yayin da daga baya zai kai ziyara Jihar Adamawa a ranar 4 ga Janairu, 2027, da kuma Legas a ranar 9 ga Janairu.
Kano na daga cikin jihohin da ake sa ran za su kasance cibiyar fafatawar siyasa a zaɓen 2027, musamman ganin cewa tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso na daga cikin manyan yan siyasar da ake adawa da APC.
A yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a Abuja, Tinubu ya bayyana cewa ba zai halarci dukkan gangaminsa ba, domin kauce wa barin ayyukan yaƙin neman zaɓe su ɗauke hankalinsa daga gudanar da mulki.
Sai dai ya ce zai ware lokaci domin yin magana kai tsaye da yan Najeriya, yayin da shugabannin jam’iyyar za su jagoranci gangamin a jihohi da ƙananan hukumomi.
Gangamin Kano zai kasance wani muhimmin mataki a ƙoƙarin APC na neman goyon bayan masu zaɓe a jihar yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
