Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karɓo bashin ƙasashen waje na dala biliyan 20.5 da kuma Yuro sama da biliyan ɗaya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar buƙatar a zaman majalisar na ranar Talata.
A cewar Tinubu, za a yi amfani da kuɗaɗen wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa, musamman a fannonin noma, ilimi, kiwon lafiya, wutar lantarki da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Majalisar Dattawa ta miƙa buƙatar ga kwamitinta mai kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje domin nazari kafin ɗaukar mataki.
