Tsohon shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci sake zaɓensa a wa’adi na biyu.
Farfesa Pakistan ya danganta matsayinsa da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Tinubu ta gudanar, da kuma abinda ya bayyana a matsayin samun ci gaba a fannin tsaro.
Sai dai rahoton jaridar Daily Trust ya mayar da hankali kan binciken ikirarin da aka danganta da Pakistan na cewa gwamnatin Tinubu ta gudanar da ayyukan da suka kai naira tiriliyan tara a Kano, inda aka ce babu hujjar da ta tabbatar da wannan ikirari.
