Gwamna Abba Kabir Yusif ya bayyana gamsuwa da yadda wakilan jihar Kano suka gudanar karatu a musabakar Alqur’ani mai girma ta kasa karo na 39 da ke gudana yanzu haka a jihar Kebbi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin mai bashi shawara na musamman kan harkar tsangaya, Gwani Musa Falaki, lokacin da yake ganawa da manema labarai a jihar ta Kebbi.
Ya ce wakilan na jihar Kano sun cancanci yabo duba da yadda suka yi karatu a matakai daban-daban tare da amsa tambayoyi daga alkalan gasar cikin kwarewa ba tare da kuskure ba.
Gwamna ya yi alƙwarin karrama wakilan na Kano da zarar sun dawo gida domin ƙarfafa musu gwiwa, tare da tabbata da ganin an daga darajar malamai da daliban da kyautata walwalar su.
Gwamna Abba ya kuma yaba wa alkalan musabakar, iyaye da kuma hukumar da ke kula da makarantun islamiyya ta Kano bisa jajircewar su a kan lamuran karatun Alqur’ani a fadin jihar.
