Shugaban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote dake Wudil, Farfesa Musa Tukur Yakasai, ya taya Farfesa Sani Lawan Manumfashi murnar naɗinsa da tabbatar da shi a matsayin Kwamishinan ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi na jihar Kano.
Farfesa Musa, wanda kuma shi ne Sarkin Kudun Gaya kuma Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Jami’o’i da Manyan Makarantun Gwamnatin jihohi a Kano, ya bayyana hakan ne daga Ƙasa Mai Tsarki, inda yake gudanar da ibadar Umrah a Saudiyya.
Ya kuma yabawa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa zaɓen Farfesa Manumfashi, tare da jinjinawa majalisar dokokin kano bisa tabbatar da naɗin, yana mai bayyana hakan a matsayin muhimmin mataki na ƙarfafa harkokin ilimi mai zurfi a Kano.
Farfesa Yakasai ya bayyana cewa ƙwarewar sabon Kwamishinan za ta taimaka wajen inganta ingancin ilimi, gudanar da manyan makarantu da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a fannin ilimi.
Haka kuma, Sarkin Kudun Gaya ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da bai wa Gwamnan Kano da Majalisar Dokokin jihar ikon gudanar da ayyukansu cikin nasara domin ci gaban Kano.
