Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya zaɓi Dr Olayemi Michael Cardoso a...

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya zaɓi Dr Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin ƙasa CBN.

Date:

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya zaɓi Dr Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin ƙasa CBN.

Zai maye gurbin tsohon dakataccen gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, da yanzu haka ke gaban kotu kan zargin cin hanci da rashawa da almundahana, zargin da ya musanta.

Dr Cardoso dai shi ne  kwamishinan tsara tattalin arziki da kasafin kudi na farko a jihar Lagos lokacin gwamnatin Bola Tinubu, Nadin na wa’adin shekaru 5, a zangon farko, zai biyo bayan amincewar majalisar dattijan ƙasar nan ne

Bayanin hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa Ajuti Ngelale ya fitar a Juma’ar nan.

Hakan nan sanarwar ta bayyana nadin mutane 4 a matsayin sabbin mataimakan gwamnan babban bankin ƙasa da suka hada da :

1. Mrs. Emem Nnana Usoro (Lagos)

2. Mr. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo (Kaduna)

3. Mr. Philip Ikeazor (Anambra)

4. Dr. Bala M. Bello (Taraba)

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...