Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMa'aikacin Premier Radio ya shiga jerin Yan Jaridu 20 da suka isa...

Ma’aikacin Premier Radio ya shiga jerin Yan Jaridu 20 da suka isa Afrika ta Kudu

Date:

Tawagar yan Jaridun Najeriya 20 ta isa kasar Africa Ta Kudu, a wani bangare na ci gaba da karbar horo da suke kan aikin jarida na zamani.

Daga cikin yan jaridun 20 din harda ma’aikacin Premier radio, Abdulrasheed Hussain, wadanda aka zaba bayan rubuta jarabawa tsakanin yan jaridu kusan dubu uku da suka fafata wajen nema.

Horan na tsawon watanni 6 an fara shi ne tin a watan Mayu, a jami’ar Pan Atlantic da ke jihar Lagos wanda kuma a yanzu suka tafi kasar Africa ta Kudu domin ci gaba da daukar horon, in da za su shafe kwanaki 10 a can.

Abdurrashid Hussain wanda Editane a tashar Premier Radio 102.7 Kano ya samu wannan nasara ne daga cikin takwarorinsa.

Kamfanin MTN ne dai ya dauki nauyin dukkan bayar da horon, karkashin wani shiri da ya bullo da shi domin karfafa aikin yan jaridu da kafafan yada labarai.

Latest stories

Related stories