Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShin da gaske ne mata a Kano basa wanka lokacin sanyi?

Shin da gaske ne mata a Kano basa wanka lokacin sanyi?

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wani bincike ya nuna yadda mata a Kano da ma saurarn sassan kasarnan ke kauracewa wanka lokacin sanyi.

A zantawar Premier Radio da wasu ‘yan mata a Kano sunce galibinsu kan kwashe kwanaki uku zuwa sati guda suna dakale a maimakon wanka.

Ko da yake al’umma na cewa lokacin sanyi lokaci ne da mata kan shiga takura ainun da hakan ke sanya su kauracewa wanka a lokuta da dama.

Amina Abubakar mai shekaru 23 da ke unguwar Na’ibawa a nan Kano ta sahidawa Premier Radio cewar da zarar lokacin sanyi ya yi , itakam ta yi sallama da wanka a kowacce rana.

Ta ce ta kan kwashe kwanaki uku a jere ba tare da wanka ba, sai dai ta dan wanke hannu da fuska ta kuma shafe su da mai.

A cewar ta da zarar sanyi ya yi tsanani to takan shafe mako guda ba tare da yin wanka ba.

“Kaga idan nayi kwaskwarima ta shikenan koda fita zanyi danasa turare na shafa hoda babu mai gane cewa banyi wanka ba.

“Kuma ni abinda yasa bana wanka sosai saboda akwai sanyi kuma gaskiya zan iya kamuwa da cutar mura matukar nace zan dinga yi kullum,” a cewar ta.

Ita kuwa wata budurwa Hajara Abdullahi mai shekaru 24 da ke Unguwar Tunkuntawa ta ce maimakon wanka takan yi kwaskawarima ne da safe ta kuma mulke jikinta da mai.

Ta ce bayan kammala aikin yamma idan taga da faraga to sai ta yi wanka.

“Na kan yi wanka lokacin sanyi amma ba da safe ba sai bayan la’asar idan nayi girkin dare sai inyi wanka.

“Sai kuma da yamma ko washe gari zan sake wanka idan naga da hali.

“Amma idan zan fita unguwa nakanyi wanka da safe kamar bayan karfe goma.

“Idan kuma sammako zanyi barin wankan nakeyi saina dawo,” Inja Hajara.

Wata budurwar kuwa ‘yar shekaru 20, mai suna Rukayya Umar da ke Rijiyar Lemo ta ce tana yin wanka sau daya a sati ne kurum.

A cewar ta musamman idan ana sanyi mai tsanani  bata ga dalilin bata lokaci wurin yin wanka ba.

Ta ce yin wanka kullum a lokacin sanyi ganganci ne, domin yin hakan kan haddasa mata ciwuka daban daban musaman cutar  Nimoniya.

“Ko da yake ban fiye fita ba idan ba makaranta zanje ba, ko da naje makarantar ma a guri daya nake zaune, shiyasa bandamu nayi  wanka ba.”

“Yin wanka lokacin sanyi yana takura min sosai. inji ta.

Ita kwa wata budurwa Hafsat Sulaiman ta ce ba ta da tsari wajen yin wanka lokacin sanyi.

“Ni bani da tsari wajen yin wanka lokacin sanyi, nakanyi wanka ne kawai idan naga rana ta fito.

“Ba a ganin alama ko kadan idan banyi wanka ba saboda yanayin sanyi baya nunawa.” A cewar ta.

Ta ce kafin shigowar sanyi tanayin wanka akalla sau uku a rana amma ba yadda ta iya dole ta rage yin wanka saboda matsalar da yin hakan kullum zai jawo mata.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories