Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar We2geda ta jan kunnen matasa kan siyasar ubangida da ta maula

Kungiyar We2geda ta jan kunnen matasa kan siyasar ubangida da ta maula

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kungiyar We2geda ta bukaci matasa a fadin kasar nan da su kaucewa siyarsar  maula da ta uban gida domin kafa kasa ingantacciyya.

Jami’in da ke jagorantar kungiyar Malam Ibrahim Abdulkarim ne ya yi kiran ya yin kaddamar da kungiyar ranar Juma’a a nan Kano.

Malam Ibrahim ya ce babbar manufar kafa kungiyar shi ne hada kan matasan Najeriya karkashi inuwa guda, su kuma samar da wani dandamali da za su taka rawa wajen gina kasa.

Ya ce kungiyar ta kunshi zaratan matasa da suka fito daga kowacce kungiyar siyasa a kasar nan, har ma da wadanda basa siyasa.

Ya kuma bukaci al’ummar kasar nan su hada hannu da wannan kungiya ba tare da la’akari da kabilanci ko banbancin addini ba wajen ceto kasar nan daga halin ha’ulain da ta shiga.

Malam Abdulkarim ya kuma ja kunnen matasa kan siyasar kudi, a cewarsa ba abinda ta ke haifarwa illa jefa matasa cikin hali ha’ula’i.

“Inason jan hankalin matasa kada su yadda a jefa su cikin siyasar daba, ko ta uban gida, ko kuma ta maula.

Haka kuma matasa da dama ne suka gudanar da jawabai a wurin taron masu cike da hikimomi, da kuma kiran matasa da su kaucewa fadawa hannun yan siyasar da za su yi amfani da su su watsar.

Latest stories

Related stories