Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan okacin da yake kaddamar da wani kwamiti mai mutane 7 wanda zai bibiyi yadda ake take dokokin tsara birane da yin gine-gine ba bisa ka’ida ba a jihar.
Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya wakilta, ya ce rashin bin dokokin tsara birane da kula da gine-gine ya zama babban kalubale a kano, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnati na samar da ingantaccen tsarin birane da bunƙasa ababen more rayuwa da kuma kyautata yanayin birnin Kano.
Alhaji Faruk ya ce an kafa kwamitin ne domin gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumar tsara biranen tare da gano dalilan da ke haddasa ci gaba da take dokokin tsara birane.
Shugaban hukumar KANGIS, Dakta Aliyu Dalhatu Sani ne zai jagoranci kwamitin, yayin da Barista Rahma Mallam Alhaji ke matsayin sakatare.
Gwamnan ya kuma umarci shugabar hukumar ta KNUPDA da daraktan sashen zane-zanen hukumar da su ajiye aikinsu na wucin gadi har sai an kammala binciken.
