Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRundunar Yan Sandan Najeriya Ta Nemi Gafarar Dan Jaridar Premier Radio.

Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Nemi Gafarar Dan Jaridar Premier Radio.

Date:

Rundunar yan sandan Najeriya ta nemi gafarar dan jaridar dake aiki da Premier Radio Muhammad Bello Dabai.

 

Wannan na zuwane bayan cin zarafinsa da wani jami’in dan sanda yayi a bakin aikinsa.

 

Rundunar ta hannun kwamishinanta na jihar Kano Mamman Dauda ta aike da tawaga ta musamman zuwa gidan Rediyo Premier karkashin mataimakin kwamishinan yan sandan Kano ACP Abubakar Modibbo.

 

Kwamishinan yan sandan na Kano ya aike da tawagar ne bayan ya bada hakuri ta wayar tarho ga hukumar gudanarwa ta Premier Radio.

 

A cikin tawagar da kwamishinan yan sandan ya aike har da jami’in da ya aikata aika-aikar, inda ya gurfana don neman afuwar Muhammad Bello Dabai.

 

Yan jarida dai na fuskantar cin zarafi daga wurin jami’an yan sanda a sassan Najeriya dama wasu sassan kasashen duniya.

 

Rundunar yan sanda ta Kano ta ce zata gudanar da bincike don daukar mataki kan dan sandan da ya ci zarafin dan jarida Muhammad Bello Dabai.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...