Rundunar Sojin kasa ta sanar da shirin ɗaukar sabbin sojoji dubu 28 bayan buɗe sabon sansanin horas da sojoji a jihar Ebonyi.
Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce sabon sansanin zai ƙara yawan sojojin da ake horaswa domin ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.
Ya ce rundunar na ci gaba da inganta ƙwarewa, samar da sabbin kayan yaƙi da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kare haɗin kan Najeriya.
Hafsan ya kuma jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa doka tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam da ƙa’idodin aikin soja.
An shirya gudanar da bikin cika shekaru 163 da kafuwar Rundunar Sojin Najeriya daga ranar 1 zuwa 6 ga Yuli a birnin Fatakwal na Jihar Rivers.
