Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Washington, inda ya ce matsalolin da Faransa ke fuskanta ba su da alaƙa da makarantu, illa shige da ficen mutane daga ƙasashen waje.
Shugaban Amurkan ya ce ya taɓa gargaɗin takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, tun shekaru da suka gabata kan abin da ya kira illolin sassauta dokokin shige da fice.
Ya ƙara da cewa Faransa ta shiga matsala ne sakamakon barin mutane da dama daga ƙasashen waje su shigo cikinta.
