Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin APC:Tsagin Shekarau ya ce sai an bashi shugaban jam’iyya zai hakura

Rikicin APC:Tsagin Shekarau ya ce sai an bashi shugaban jam’iyya zai hakura

Date:

Mukhtar Yahya Usman

A yayin da rikicin cikin gida a jam’iyyar APC a nan Kano ke dada daukar dumi tsagin tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce sai an bashi shugabancin jam’iyyar sannan zaihakura.

Haka kuma tsagin ya ce baya ga shugabancin jam’iyyar an tabbatar masa da kaso 55 na mukaman da za a raba.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da uwar jami’iyyar ta kasa ta fitar da matakan sulhu ta kuma sanya gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci sulhun.

Sai dai a cikin wata sanarwa da tsagin na Shekarau ya fitar mai dauke da kwanan watan 10 ga Fabrairun da muke ciki ya yi watsi da matakin uwar jam’iyyar ta kasa.

Sanarwar ta ce sunanan akan bakansu na sai an basu shugabancin jam’iyya da kuma kaso 55 na mukaman da ake da su, kafin su tabbatar an dai-daita.

Haka kuma sunce babu yadda za a yi su lamunci cewar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne zai jagoranci kwamitin Sulhun.

A cewarsu babu yadda za a yi kana kai ruwa rana da mutum kuma a ce shi ne zai jagoranci zaman Sulhu.

Sun kuma bukaci indai za a tattauna da su to sai gwamana Ganduje ya janye daukaka karar da ya yi akan hukunci kotu da ta basu nasara.

Latest stories

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...

Related stories

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...