Abubakar Haruna Galadanci
A yayin da aka ci gaba da zaman kotun kan shari’ar kisan kan da aka yiwa hanifa, wanda ake zargi da kisan ya musanta aikata hakan a gaban kotu.
A zaman kotun na yau Litinin karkashin mai shari’a Usman Na’abba, Abdulmalik Tanko ya ce kokadan ba shi ya kasheta ba kuma bashi da masaniya kan aikata hakan.
Idan za a iya tunawa dai Abdulmalik ya amsa kisan Hanifa bayan da rundunar ‘yan sanda ta yi holinsa a shalkwatarsu.
Har ma ya bayyana cewar ya kasheta ne da shinkafar bera ta N100 bayan da ya saceta ya kuma boyeta a wani wuri.
Sai dai bayan da aka gurfanar da shi a gaban babbar kotun jiha ranar litinin ya ce ko kadan bai aikata kisan kanba.
Wannan ce ta sanya alkalin kotun ya dage shari’ar har zuwa ranar 2 da 3 ga Maris mai kamawa domin sauraron karar, ya kuma bayar da umarnin a ci gaba da tsareshi a gidan yari.