Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar 15 ga Disamba, 2026, domin wallafa cikakken jerin sunayen masu rajistar zaɓe gabanin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan yayin wani taro da jami’an INEC a birnin Fatakwal na Jihar Ribas.
Amupitan ya ce hukumar na gudanar da bincike kan zargin shigar da hotunan bogi da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar basirar wucin gadi (AI) cikin rajistar masu zaɓe ta wucin gadi.
Ya buƙaci ƴan Najeriya da su duba sunayensu a rajistar, tare da kai rahoton duk wani kuskure ko bayanan da ba su dace ba domin a gyara su kafin zaɓen.
Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa hukumar na ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen zaɓen 2027, ciki har da shirin samar da na’urorin tantance masu zaɓe na BVAS guda dubu 57.
Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da laifin kai hari ga jami’an zaɓe ko ma’aikatan hukumar zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
