Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRabon dabbobi dubu biyar ga ’yan gudun hijira a garin Pulka da...

Rabon dabbobi dubu biyar ga ’yan gudun hijira a garin Pulka da ke yankin karamar hukumar Gwoza – Gwamnatin Borno

Date:

Gwamnatin Borno da hadin gwiwar kungiyar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya ta fara rabon dabbobi dubu biyar ga ’yan gudun hijira a garin Pulka da ke yankin karamar hukumar Gwoza

Babban sakataren ma’aikatar raya karkara Alhaji Yusuf, ya ce ma’aikatar ta raba awaki da tumaki 3,000 ga mata 500, sannan za a raba karin 200 kafin karshen wannan shekara.

Ya ce hakan wani kokari ne na dawo da al’ummomin da suka rasa muhallansu zuwa gida, tare da rage radadin talauci, da ba su abun dogaro da kansu.

Da yake kaddamar da rabon, mataimakin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur, ya ce wani bangare ne na shirin gwamnati na raya jihar na shekaru 25, ta hanyar tsare-tsaren shekaru goma.

Ya kara da cewa, gwamnatin za ta ci gaba da amfani da dabarun inganta rayuwar al’ummar jihar, ciki har da ta hanyar hada kai da abokan huldar ci gaba domin samun kyakkyawan sakammako.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...