
Kungiyar Masu Kiwon Kaji ta Najeriya reshen jihar Kano ta bukaci gwamnatin tarayya da ta jiha da kuma masu hannu da shuni da su ceto masana’antar kiwon kaji daga durkushewa sakamakon barkewar cutar murar tsuntsaye a jihar.
Kiran na cikin wata sanarwa ce da shugaban kungiyar, Dakta Usman Gwarzo ya fitar a hannu a ranar Laraba.
Kungiyar ta bayyana damuwarta matuka game da irin asarar da masu kiwon suka fuskanta daga watan Nuwamba 2024 zuwa Fabrairu 2025, inda aka samu mutuwar dubban kaji sakamakon cutar Murar Tsuntsayye ta ‘Avian Influenza’.
“Masana’antar kiwon kaji na taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci da aikin yi, amma har yanzu ana nuna sakaci wajen kareta daga irin wannan barazana,” in ji Dakta Gwarzo.
Kungiyar ta ce, yayin da gwamnati ta hanzarta daukar mataki kan gobarar da ta faru a wata kasuwa kwanan nan, an nuna lissafi da watsi da harkar kiwon kaji wadda ke tallafawa dubban iyalai a jihar.
Ta kuma jaddada cewa wannan rashin daidaito ya kara bayyana bukatar gyara da karfafa tsarin bayar da agaji a fannin noma da kiwo.
Sannan kungiyar ta bukaci gaggawar tallafin kudi da shirin farfado da masana’antar tare da samar da manufofi masu dorewa da za su bai wa manoma damar tashi daga asarar da suka fuskanta.
Sun ce hakan zai taimaka wajen hana kara tabarbarewar tattalin arzikin yankin da kasa baki daya.
A halin yanzu, Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da barkewar cutar murar tsuntsaye a Kano, tare da daukar matakan wayar da kai da kuma kara tsaurara tsaro a fannin lafiyar dabbobi don dakile yaduwar cutar.