Rundunar ’yan sandan Jihar Kogi ta yi alƙawarin samar da ingantaccen tsaro tare da bai wa dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu damar gudanar da harkokinsu cikin ’yanci da adalci yayin zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Naziru Bello Kankarofi, ne ya bayyana hakan, inda ya ce rundunar ta shirya tsaf domin tabbatar da zaman lafiya kafin zaɓen, lokacin gudanar da shi da kuma bayan kammala zaɓen.
Ya bayyana cewa ya gana da shugaban Hukumar Zaɓen Ƙananan Hukumomin Jihar Kogi (KOSIEC), Mamman Nda-Eri, domin tattauna shirye-shiryen tsaro da matakan da za a ɗauka don tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana.
Rundunar ta kuma gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji tayar da hankali, amfani da ’yan daba, yaɗa kalaman ƙiyayya da duk wani aiki da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya a lokacin zaɓen.
Za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Kogi a ranar 17 ga Oktoba, 2026, a ƙananan hukumomi 21 na jihar.
A nasa ɓangaren, shugaban hukumar KOSIEC, Mamman Nda-Eri, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da sauran masu ruwa da tsaki da su gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da bin dokokin zaɓe domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
