Gwamnatin Kano ta sanar da samun ci gaba wajen rage mace-macen mata masu juna biyu, wanda adadin ya sauka daga 1,025 cikin haihuwa 100,000 a shekarar 2025 zuwa 570 a halin yanzu.
Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da cibiyar lafiya ta matakin farko a Gadon Kaya da aka sabunta karkashin shirin IMPACT mai samun tallafin Bankin Duniya.
Farfesa Salisu Ibrahim ya ce nasarar ta samo asali ne sakamakon haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kano da gwamnatin tarayya har ma da abokan hulɗar ci gaba, inda aka sabunta sama da cibiyoyin lafiya 350 ta hanyoyin shirye-shiryen da suka haɗa da IMPACT, LAFIYA, UNICEF da sauran su.
Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano, ya kuma bayyana cewa an gyara tare da inganta sama da cibiyoyin lafiya 500 a faɗin jihar nan, lamarin da ya taimaka wajen ƙara ayyukan kiwon lafiya da kuma bunƙasa rigakafin yara.
A nasa ɓangaren, Manajan Shirin IMPACT, Dakta Nura Ganduje, ya ce sabunta cibiyar lafiya ta Gadon Gaya na daga cikin cibiyoyi 187 da aka inganta a jihar nan.
Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya da abokan hulɗarta za su ci gaba da tallafawa harkokin kiwon lafiya domin rage mace-macen mata da kuma kananan yara a jihar Kano.
