Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rijistar jarabawar kammala sakandire ta NECO da WAEC domin ba da damar gudanar da ƙarin tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ta ce ta janye wasiƙar da ta fitar a ranar 18 ga Yuni, 2026, wadda ta sanar da shirin ƙara kuɗin rajistar.
A cewar ma’aikatar, an ɗauki wannan mataki ne bayan damuwa da ra’ayoyin da jama’a suka bayyana game da shirin ƙara kuɗin.
Ma’aikatar ta bayyana cewa tun farko an shirya ƙarin kuɗin ne saboda hauhawar kuɗaɗen gudanar da jarabawa, ciki har da sufuri, tsaro, buga takardun jarabawa, amfani da fasaha, tabbatar da inganci da sauran muhimman ayyuka. Ta kuma ce kuɗin rajistar bai samu ƙarin farashi ba tsawon shekaru duk da hauhawar kuɗin gudanar da waɗannan ayyuka.
Sai dai Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ya ba da umarnin dakatar da shirin domin a gudanar da cikakkiyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki, bisa manufar gwamnatin tarayya ta yin tsare-tsaren da suka haɗa kowa da kowa, tare da bayyana gaskiya da kuma dogaro da hujjoji.
Ma’aikatar ta ce wannan mataki ya nuna ƙudirin gwamnati na tabbatar da cewa duk wata manufa da za ta shafi miliyoyin ɗalibai da iyalansu an yi nazarinta sosai kuma ta dace da muradun ƙasa.
Ta ƙara da cewa za a gudanar da tattaunawa da hukumomin shirya jarabawa, ma’aikatun ilimi na jihohi, masu makarantu, ƙungiyoyin iyaye, ƙungiyoyin ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki kafin a yanke hukunci na ƙarshe.
Ma’aikatar ta jaddada cewa ba za a fara aiwatar da ƙarin kuɗin rajistar ba har sai an kammala wannan shawarwari da tattaunawa.
Haka kuma ta tabbatar wa yan Najeriya cewa jin daɗin ɗalibai, samar da damar samun ingantaccen ilimi ga kowa da kuma tsara manufofi masu anfani suna ci gaba da kasancewa cikin manyan abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanya a gaba.
