Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiNNPC zai fara fitar da tataccen man fetur don siyarwa ƙasashen waje...

NNPC zai fara fitar da tataccen man fetur don siyarwa ƙasashen waje daga watan Disamba.

Date:

Shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC) Mele Kyari ya ce alamu sun nuna cewa Najeriya zata rinka fitar da tataccen manfetur daga watan Disamba.

Kyari, ya bayyana hakane a Litinin din nan a gaban kwamitin kudi na majalisar dattijan kasar nan.

Yayin da yake jawabin yana tare da ministan kudi Wale Edun, dana kasafin kudi Atiku Bagudu da gwamnan bankin kasa CBN Olayemi Cardoso da sauran masu ruwa da tsaki.

Kyari ya ce alamun dake nuna kasar nan zata fara fitar da manfetur sun hada da matatar mai ta Fatakwal da zata fara aiki a watan gobe da matatun man Warri da Kaduna da zasu fara aiki nan bada jimawa ba.

Ya kara da cewa nan bada dadewa ba man da ake fitarwa zai karu zuwa ganga miliyan 2 a kowace rana wanda kuma tuni an dauki hanyar yin hakan.

Da yake jawabi ministan kasafin kudi da tsare-tsare Atiku Bagudu, y ace tuni kasafin kudin 2024 ya fara aiki kuma ana cigaba da tattaunawa da kungiyar kwadago kan mafi karancin albashi don tabbatar da cewa ba a sake samun tasgaro ga tattalin arziki ba.

Ya kuma bukaci alumma dasu cigaba da hakuri yayin da gwamnati ke cigaba da aiki don farfado da tattalin arziki.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...