Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaNajeriya ta bayyana rashin ji dadin ta game da ficewar kasashen...

Najeriya ta bayyana rashin ji dadin ta game da ficewar kasashen Nijar da Mali da Burkinafaso sukayi daga ECOWAS.

Date:

Nijeriya ta bayyana bakin cikinta dangane da sanarwar da kasashen Nijar, Mali da Burkinafaso suka dauka na ficewa daga kungiyar hadin kan kasashen Afrika ECOWAS.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya Francisca K. Omayuli (Mrs) ce ta fitar da sanarwar.

Kasar nan wadda take zama babbar Jigo da ma rikon shugabancin ECOWAS ta dage wajen ganin an dawo da mulki hannu farar hula tare da sakin hambararren tsohun shugaban kasar Nijar Bazoum Muhammad.

Kazakika sanarwar ta kara da cewa Nigeria ta Kasan ce tana tuntubar dukkan kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS domin warware matsalolin da ake fuskanta a kasashen da akayi juyin mulki.

haka zalika Najeriya na ci gaba da bude kofa ga kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar, ta yadda daukacin al’ummar yankin za su ci gaba da cin moriyar tattalin arziki da kimar dimokradiyya da kungiyar ECOWAS ta amince da su.

A karshe Najeriya ta kara yin kira ga kasashen duniya da su ci gaba da bayar da goyon baya ga kungiyar ECOWAS da kuma hadin gwiwa da hadin kai.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...