Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMun shirya gurfanar da gwamnatin tarayya gaban shari’a dangane da harin da...

Mun shirya gurfanar da gwamnatin tarayya gaban shari’a dangane da harin da sojojin tarayya suka kai kan masu bikin maulidi a Kaduna – Kungiyar lauyoyi ta ‘Concerned Northern Lawyers Forum’

Date:

Kungiyar lauyoyin nan ta ‘Concerned Northern Lawyers Forum’ mai rajin kare martabar arewa ta ce ta shirya gurfanar da gwamnatin tarayya gaban shari’a dangane da harin da sojojin tarayya suka kai kan masu bikin maulidi a garin Tudunbiri da ke yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Daya daga cikin mambobin kungiyar, Barista Zurkallaini Sani Tsanyawa ya bayyanawa Premier Radio bayan wani taronsu a karshen makon jiya cewa, za su tabbatar da ganin sun kwatowa wadanda abun ya rutsa dasu hakkinsu musamman ta hanyar biyan diyya.

Barista Zurkallaini ya ce dama sun kafa kungiyar ce saboda irin abubuwan da ke faruwa a Arewa na ta’addanci, musamman ganin yadda gwamnati ke kokari wajen samar da kayan aiki da horo ga jami’an tsaro, amma sakaci da ganganci daga jami’an na haddasa matsaloli.

Lauyan na kungiyar ‘Concerned Northern Lawyers Forum’ ya ce burinsu shi ne ganin sun kwatowa ‘yan arewa hakkinsu a ko da yaushe.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...