Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dinkin duniya na shirin sake aiwatar da wani taron gaggawa domin...

Majalisar dinkin duniya na shirin sake aiwatar da wani taron gaggawa domin duba yiwuwar kada kuri’ar amincewa da tsagaita wuta a Gaza.

Date:

Majalisar dinkin duniya na shirin sake aiwatar da wani taron gaggawa domin duba yiwuwar kada kuri’ar amincewa da tsagaita wuta a Gaza.

Wannan sabon yunkuri ya zo daidai lokacin da farar hula ke dada rasa rayuka sanadiyyar ruwan wutar da Isra’ila ke yi a sassa daban-daban na yankin.

Ko a makon jiya sai da majalisar dinkin duniya ta gudanar da makamancin wannan taro, amma Amurka ta hau kujerar naki game da tayin tsagaita wuta a Gaza, al’amarin da ya sa aka tashi taron ba tare da cimma matsaya ba.

A jawabin da suka gabatar, wakilan tawagar kwamitin tsaro na majalisar sun tabbatar da irin tashin hankalin da al’ummar Gaza ke ciki musamman ganin babu wani tudun mun tsira yanzu haka a yankin.

Da yake amsa tambayar manema labarai, wakilin kasar China a tawagar, Zhang Jun, ya ce tura ta kai bango, saboda haka lokaci ya yi da ya kamata a tsagaita wuta haka.

Kusan dukannin kasashe mambobin majalisar dinkin duniya sun goyi bayan tsagaita wuta, in banda Amurka da ke ganin har yanzu Isra’ila na daukar Fansa kan harin da Hamas ta kai kasar watanni biyu da suka kamata.

Latest stories

Related stories