Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kashe wani jami’in soja, mafarauci da mace mai juna biyu, tare da sace wasu mazauna yankin Karim-Lamido a Jihar Taraba.
Maharan sun kai farmakin ne a ranar Talata a ƙauyukan Kuka Sarkin Yamma da Ruwan Zafi, inda suka kuma raunata wani soja.
Wani shugaban al’umma a yankin, Tanko Bobbo Andami, ya bayyana cewa sojoji da mafarauta sun fafata da maharan, inda suka yi nasarar ceto mutum biyar daga cikin waɗanda aka sace.
Ya ce har yanzu akwai mutum 15 a hannun maharan, ciki har da mata da yara.
Harin na zuwa ne ƙasa da makonni biyu bayan wani mummunan hari da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a garin Binnari da ke ƙaramar hukumar.
Ya zuwa lokacin haɗa rahoton, rundunar ƴansandan Jihar Taraba ba ta fitar da sanarwar hukuma kan sabon harin ba.
