Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaMinistan shari’a na kasa Lateef Fagbemi ya ce yajin aikin da ƙungiyoyin...

Ministan shari’a na kasa Lateef Fagbemi ya ce yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka fara a yau ya saɓa wa doka.

Date:

Ministan shari’a na kasa Lateef Fagbemi ya ce yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka fara a yau   ya saɓa wa doka.

Yace kungiyoyin basu bi ka’idojin da dokar ƙwadago ta gindaya ba, kamar yadda tashar talabijin ta Channels ta ruwaito.

Ƙungiyoyin ƙwadagon na son a sanya albashi mafi ƙanƙanta kan naira dubu 494, yayinda gwamnati ta toke kan naira dubu 60.

A gefe guda wakilan NLC da TUC sun rufe hanyar shiga babban ofishin kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) da ke Abuja.

Yanzu haka dai ana cikin hali na rashin tabbas kan tasirin da yajin aikin zai yi, sai dai ana fargabar zai iya tsayar da al’amura a faɗin ƙasar.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...