Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaKungiyoyin kwadago sun kashe manyan turakun lantarki na Najeriya.

Kungiyoyin kwadago sun kashe manyan turakun lantarki na Najeriya.

Date:

Kungiyoyin kwadago sun kashe manyan turakun lantarki na Najeriya.

A cikin wata sanarwa da kamfanin rarraba lantarki na ƙasa TCN ya fitar, ya ce tun da karfe 02:19 na dare yan kwadago suka kashe manyan turakun lantarkin da gangan, abinda ya jefa kasar nan cikin duhu.

Sanarwar ta ce an kori duk ma’aikatan dake aiki wurin da ake rarraba lantarki a Benin tare da lakaɗawa wasu ma’aikata dukan kawo wuka da jiwa wasu rauni.

Hakan ya sa manyan turakun lantarki na Benin suka ɗauke ɗuf.

Sauran wuraren manyan turakun lantarki na Najeriya da ƴan kwadago suka kashe sun haɗa da Ganmo da Ayede da Olorunsogo da Akangba da Osogbo.

Wannan na faruwa yayin da aka shiga rana ta farko a yajin da yan kungiyar kwadago suka daka yau litinin.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories