Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce rashin fahimtar kyawawan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin shugaban Bola Ahmed Tinubu ne, yasa wasu daga cikin ‘yan Najeriya suke bayyana mabanbantan ra’ayi da sanya kokwanto a zukatan su game da mulkin Shugaban da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke gudanarwa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron fidda gwanin dan takarar Shugaban kasa ta hanyar ‘yar tinke ta jam’iyyar APC ta gudanar a mazabar gwamnan ta Diso dake ƙaramar hukumar Gwale.
Gwamna Abba ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta zo da tsare-tsare masu amfani musamman a ɓangaren tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da kuma ƙoƙarin dawo da martabar Najeriya a idon duniya.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar APC na ci gaba da samun karɓuwa a sassan Najeriya sakamakon yadda gwamnoni da shugabannin jam’iyyar ke haɗa kai wajen tabbatar da cigaban ƙasa da walwalar al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa gwamna Abba Kabir Yusuf, shi ne wakilin shugaban kasa wato ‘’Agent’’ a jihar Kano kuma ya jagoranci taron ne a matsayin jagoran mazabar ta sa, kamar yadda aka gudanar da irin taron a dukkanin ƙananan hukumomin Najeriya.
