Premier Radio 102.7 FM
Kano Labarai

Max Air ne zai yi jigilar mahajjatan Kano a bana

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa jirgin Max Air ne zai yi jigilar Alhazanta zuwa kasa mai tsarki a bana.

Babban sakataren hukumar Jin dadin Alhazai na Kano Muhammad Abba Danbatta ne ya tabbatar da hakan yayin taron manema Labarai ranar Lahadi.

Ya ce bayan dogon nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki yanzu an tabbatar da Jirgin Max Air a matsayin wanda zai yi jigilar alhazan Kano.

Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne dai Kamfanin Azman Air ya ce hukumar NAHCON  ta bashi damar ya yi jigilar Alhazan Kano.

Sai dai hukumar Jin dadin Alhazai ta Kano ta ki amincewa da baiwa Kamfanin dama.

Inda ta ce Shekara da shekaru ta na aiki ne da Kamfanin Max Air kuma bai taba Basu matsala ba, babu dalilin da zai sa su yi watsi da shi.

A Wani Labarin...

Buhari zai cefanar da kadarorin gwamnati 42

Mukhtar Yahya Usman

Ganduje zai yiwa gadar Kofar Ruwa kwalliyar Milyan 500

Mukhtar Yahya Usman

Ba jami’in mu ne ke shan giya a wani faifan bidiyo ba- KAROTA