Premier Radio 102.7 FM
Kiwon Lafiya Labarai

YUMSUK: ta kaddamar da cibiyar gwajin cutar kansar mahaifa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule dake nan Kano, (YUMSUK) ta kaddamar da cibiyar binciken gano kansar bakin mahaifa a tsakanin mata a yankin Arewacin kasar nan.

A zantawarta da Premier Radio, Jami’a mai kula da cibiyar, kuma kwararriyar likita bangaren mata ta jami’ar, Dakta Iman Usman Haruna, tace cibiyar zata gudanar da gawaje-gwaje kan mata dubu daya da dari biyar daga jihohin Kano, Jigawa, Katsina.

Majalisa ta tadakatar da gina shaguna a jikin asibitin Zana a nan Kano
Tace cutar kansar bakin mahaifa na damun mata da dama a wannan yanki ba tare da sun sani ba, inda tace ana samun cutar ne ta hanyar mu’amalar aure.

Dakta Iman Usman Haruna ta ce wannan gwajin kyauta ne, kuma ana fatan zurfafa bincike domin samu waraka tsakanin matan.

A Wani Labarin...

Sunayen wadanda jam’iyyar NNPP ta zaba a matsayin shugabanninta

Mukhtar Yahya Usman

Max Air ne zai yi jigilar mahajjatan Kano a bana

Mukhtar Yahya Usman

Jirgin Qatar ya fara suka a Kano

Mukhtar Yahya Usman