Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta amince da ƙudurin kafa rundunar ’yan sandan jihohi.
Shugaban Majalisar Isma’ila Zannan Moriki ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa ’yan jarida jawabi a wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishinsa a yammacin jiya Litinin.
Ya ce ƙudurin ya biyo bayan aikawa majalisun dokokin jihohi da Majalisar Ƙasa ta yi da wasu shawarwarin sauye-sauyen Kundin Tsarin Mulki domin su duba tare da yanke shawara a kansu.
A cewarsa, idan aka amince da kafa rundunar ’yan sandan jihohi, hakan zai samar da ƙarin taimako wajen tunkarar matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Zannan Moriki ya kuma yi watsi da zargin cewa wasu sauye-sauyen siyasa na baya-bayan nan da suka shafi wasu ’yan majalisar sun kawo cikas ga ayyukan majalisar.
