Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dattawa ta ce matakin da 'yan kwadagon suka dauka na kashe...

Majalisar dattawa ta ce matakin da ‘yan kwadagon suka dauka na kashe manyan turakun lantarki a kasar nan tamkar zagon kasa ne.

Date:

Majalisar dattawa ta kasar nan ta ce matakin da yan kwadagon suka dauka na kasha manyan turakun lantarki a kasar nan tamkar zagon kasa ne ga tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban majalisar dattawa na kasar nan ya nuna damuwa matuka kan matakan da suka biyo bayan yajin aikin kungiyoyin kwadago wanda ya hadasa kashe manyan turakun dake bawa kasar nan wutar lantarki, da kuma jefa masu tafiya aikin hajji a kasar nan cikin damuwa

Shuagabn majalisar dattawan Sanata Godswill Akpabio ya fadi haka lokacin da yake jagorantar zaman majalisar dattawa a Talatar da ta gabata, ya ce matakin da yan kwadagon suka dauka tamkar zagon kasa ne ga tattalin arzikin Najeriya.

Wannan martini na shugaban majalisar dattawan na zuwa bayan da sanata Diket Plang ya gabatar da wani kuduri kan batun mafi karancin albashi wanda yan majalisar suka tafka muhawara a kai.

Shugaban majalisar dattawan ya kuma yiwa kungiyoyin kwadago na NLC da TUC alkawarin cewa majalisar zata yi dukkanin mai yuwuwa domin ganin kudirin mafi karancin albashin da suke jira ya fara aiki.

Latest stories

Related stories