Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin Jihar Neja, ta ce rashin tsaro ya kawo cikas ga aikin...

Gwamnatin Jihar Neja, ta ce rashin tsaro ya kawo cikas ga aikin ceto mutum 30.

Date:

Gwamnatin Jihar Neja, ta ce rashin tsaro ya kawo cikas ga aikin ceto mutum 30 da suka maƙale a mahaƙar ma’adinai da ta rufta a Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ya ce hukumar ba ta samu cikakkun bayani kan adadin da aka ceto ba saboda rashin tsaro a yankin.

Babban daraktan, ya kuma ce hukumar ta samu rahoton yadda ’yan bindiga ke kai hare-hare a yankunan Shiroro da Mashegu a jihar.

Ya nuna damuwarsa kan yadda masu ceto suka tsere daga wajen sakamakon ci gaba da rufatawa da ramukan ke yi.

Amma ya ce an tura mutane masu aikin haƙar ma’adinai a yankin domin gudanar da aikin ceto.

Yana wannan batu bayan wani rahotanni ya tabbatar da mutum guda yayin da wasu da dama suka maƙale a mahaƙar ma’adinai dake Shiroro da ke Jihar Neja.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...