Gwamnatin Kano ta yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga taron ƙasa na ƙungiyar ƙwararrun masu hulɗa da jama’a ta Najeriya, NIPR, wanda za’a gudanar a Abuja daga ranar 15 zuwa 21 ga Nuwamba 2026.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi tawagar shugabanni da mambobin NIPR a Gidan Gwamnatin Kano.
Gwamna Abba wanda daraktan yaɗa labaran sa Sunusi Bature D/Tofa ya wakilta, ya ce Gwamnatin ta kuma amince da tallafawa ƙungiyar wajen samar da fuloti domin gina ofishinta a Kano, tare da ci gaba da samar da damar horaswa da bunƙasa ƙwarewar sabbin masu aikin.
A nasa jawabin, tsohon Shugaban NIPR na ƙasa, Farfesa Sule Ya’u Sule, ya ce taron zai tattauna sabbin sauye-sauye da abubuwan da ke faruwa a fannin hulɗa da jama’a, tare da duba yiwuwar sake fasalta ma’ana, ka’idoji da salon aikin hulɗa da jama’a, waɗanda aka samar tun a wani taro da ƙungiyar ta gudanar a birnin Mexico a shekarar 1978.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sunusi Bature na cewa gwamnatin Kano a shirye take ta haɗa gwiwa da NIPR wajen horas da sabbin ƙwararru da kuma sake horas da waɗanda ke aiki a fannin, musamman kan bin ƙa’idojin hulɗa da jama’a.
