Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAn samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

Date:

An samu rabuwar kai a
Jamiyyar PDP

na bayyana cewa, An sami rarrabuwar kai a babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP a nan jihar Kano, a dai dai lokacin da jamiyyar ke tunkarar zaben shugabannin mazabu da Deliget wato wakilan jamiyyar wadanda za su wakilci kananan hukumomin jihar nan a wajen babban taron jamiyyar na Kasa.

Uwar jamiyyar ta kasa tuni ta bayar da sanarwar cewa a sati mai zuwa wato ranar Asabar 27 ga wannan wata na Yuli, jam’iyyar ta PDP zata gudanar da zaben shugabanni a duka mazabu na kananan hukumomi dake kasar nan gaba daya.

To sai dai anan Kano, shirin zaben ya haifar da rabuwar jamiyyar zuwa tsagi biyu, kuma kowanne gida ke kallon shi ne ya kamata ya zama jagoran jamiyyar anan Kano.

Bangare na farko shine gidan Ambasada Aminu Wali, wato gida na farko ke nan na jamiyyar wanda yake da Ambasada Aminu Wali a matsayin jagora, kuma wannan gida sami goyan bayan tsohon dan takarar gwamna, Alh. Ibrahim Little da mukarraban sa, da kuma Sadiq Wali da Yusuf Dambatta wadanda sune jam’iyyar ta tsayar a matakin ‘yan takarar gwamna da mataimakinsa a zaben da ya wuce.

Yayin da daya bangaren na PDP shine na Gidan Sanata Bello Hayatu Gwarzo wanda shi Bello Hayatun yake jagoranta. Wannan gida, kuma tuni ya hade da ‘Yan Shura wato mutanen tsohon gwamna Malam İbrahim Shekarau da ⁠’Yan Maslaha a karkashin tsohon kwamishina Yusuf Ado Kibiya, sai kuma yan Reformation Group wato mutanen da Dr Dangwani yake shugabanta.

A yanzu dai an ja daga, daidai lokacin da kowane sashe cikin biyun ke ci gaba da tuntubar juna da kuma tsara shirye shiryen shiga zaben da za’ayi sati mai zuwa.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muĈ™aminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muĈ™aminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...