Ƙungiyar ƙwadago ta kasa, NLC, ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni 2 da ta rage farashin man fetur tare da fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu, bayan taron haɗin gwiwa na majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) da kwamitin gudanarwa (CWC), da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
NLC ta buƙaci gwamnati ta rage farashin man fetur zuwa matakin da yake a lokacin da aka sanya hannu kan dokar mafi ƙarancin albashin naira dubu 70 a shekarar 2024, ƙungiyar ta ce tashin farashin fetur da faɗuwar darajar naira sun rage ƙarfin kuɗin ma’aikata, har suna fuskantar wahalar biyan bukatun yau da kullum kamar abinci, haya, sufuri, lafiya da ilimi.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci a fara tattaunawar sabon albashi kafin ƙarshen watan Oktoba, tare da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya na JOHESU, da kuma buƙatun kwamitin tattaunawar ma’aikatan gwamnati ta kasa, ta kuma nemi a samar da rangwamen haraji ga ma’aikata da biyan alawus na tallafi domin rage tasirin tsadar rayuwa.
NLC ta ce wa’adin zai fara aiki daga ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, kuma ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza cika buƙatunta cikin makonni biyun, za ta ɗauki matakan da shugabannin ƙungiyar za su amince da su.
