Majalisar dattawan ƙasar nan ta bayyana kwarin gwiwar cewa aƙalla majalisun dokokin jihohi 24 za su amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar domin kafa rundunonin ’yan sanda na jihohi.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan yaɗa labarai da harkokin jama’a, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar The Punch, ya ce majalisar na sa ran samun amincewar da ake buƙata domin ci gaba da tsarin kafa ’yan sandan jihohi.
An aika da kudirin ga majalisun dokokin jihohi 36 a ranar 16 ga Satumba, 2026, domin su yi nazari tare da bayyana matsayinsu, a ƙarƙashin tanadin kundin tsarin mulki, ana buƙatar amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun jihohin, wato jihohi 24, kafin gyaran ya samu damar ci gaba.
Sai dai ya zuwa ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, jihohi huɗu ne kawai Edo, Oyo, Osun da Rivers, suka amince da kudirin, hakan na nufin ana buƙatar ƙarin jihohi 20 domin cimma adadin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Adaramodu ya kuma ce yana da yakinin cewa za’a kammala wannan tsari a zaman majalisa ta goma, kafin majalisa ta goma sha ɗaya ta fara aiki, ana sa ran majalisun jihohin za su mayar da martaninsu nan da mako mai zuwa, duk da cewa har yanzu ba a kai ga samun amincewar da ake buƙata ba.
