Yayin da ake ci gaba da cece-cuke kan batun samar da ‘yan sandan jihohi, gwamnatin Kano ta ce ta shirya tsaf domin samar da ‘yan sandan a wani mataki na karfafa tsaron cikin gida.
A cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf, rundunar za ta yi aiki ne kafada da kafada da yan sandan tarayya, wajen murkushe nau’in matsalar tsaron da ke addabar jihar Kano.
Fadan daba, kwacen waya, da shaye shaye su ne manyan matsalolin tsaro da jihar Kano ke fusktanta a daidai wanda lokaci, wanda al’umma ke ganin cewa manyan hukumomin tsaro sun kasa magance matsalolin.
Ko ta wadanne hanyoyi yan sandan jihar za su taimaka wajen dakile wadannan matsaloli a Kano?
Premier Radio ta tattauna da wani mi sharhi kan harkokin tsaro Abdullahi Bakoji mai ritaya, wanda ya bayyana cewa samar da ‘yan sandan jihohi abu ne mai kyau matukar an yi tsarin da ya dace wajen bayar da horo, samar musu da kayan aiki da kuma walwalar ma’aikata.
Ya kara da cewa ‘yan sandan za su iya taimakawa wajen rage fadan daba da kwacen waya a ciki da wajen Kano, kaancewar ma’aikatan da za dauka ‘yan garin ne kuma zasu kasance suna da sanayyar masu aikata laifuka da wuraren da suke aikata laifin.
Abdullahi Bakoji mai ritaya ya jaddada cewa dole sai an yi samu hadin kai tsakanin ‘yan sandan tarayya dana jihohi da sauran hukumomin tsaro za a iya magance matsalolin da ke addabar jihar Kano da ma kasa baki daya.
