Hukumar Kwashe Shara ta jihar Kano REMASAB, za ta samar da makamashi daga sharar mayankar Kano da sauran sharar da ke ruɓewa ta hanyar sarrafa su zuwa iskar biogas da wasu nau’ikan makamashi mai sabuntawa.
Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Abubakar Ahmad, ya fitar a ranar Laraba, 30 ga Satumba, 2026.
Ya ce, Hukumar ta tattauna da Mr. Paul na Kamfanin Raphia Green Ltd. kan shirin, wanda za a yi amfani da fasahar sarrafa sharar da ke ruɓewa ba tare da iskar oxygen ba domin samar da makamashi.
Sanarwar ta ce, Shugaban Hukumar, Dakta Muhammad S. Khalil, ya ce amfani da fasaha da haɗin gwiwa na daga cikin hanyoyin da hukumar ke bi wajen samar da tsarin sarrafa shara mai ɗorewa kamar yadda jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Abubakar Ahmad ya bayyana
