Umahi ya bayyana hakan ne a yayin taron shugabannin jam’iyyar APC a Kano, inda ya yaba da matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin tabbatar da tsaftar muhalli da kare lafiyar al’umma.
Ministan, wanda ya ziyarci Kano gabanin ƙaddamar da aikin hanyar Kaduna zuwa Kano, ya ce tsaftar muhalli na da muhimmanci wajen inganta lafiyar jama’a da kyautata rayuwarsu.
Ya kuma yaba da shirin Operation Kano Tsaf-Tsaf, wanda gwamnatin jihar ta ƙaddamar domin ƙarfafa tsaftar muhalli da wayar da kan jama’a kan yadda ya kamata su kula da wuraren da suke zaune.
Umahi ya bukaci sauran jihohi da su rungumi irin waɗannan matakai, tare da jaddada cewa samun tsaftataccen muhalli na buƙatar haɗin gwiwar gwamnati da al’umma.
