Gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa, ya ce har kawo yanzu ba’a samu wani mai rai ba bayan da jirgin saman rundunar sojin saman kasar nan ya yi hatsari a Igbokoda, ƙaramar hukumar Ilaje ta jihar.
Aiyedatiwa ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce mazauna yankin, jami’an tsaro da jami’an agaji sun gudanar da bincike a wurin hatsarin, amma ba su samu wani mutum da ke raye ba.
Gwamnan ya ce an gano wasu tarkacen jirgin, ciki har da sassan fuka-fukansa, katunan shaida da kayan sawa, lamarin da ya tabbatar da cewa jirgin na soja ne.
Rundunar sojin saman dai ta tabbatar da cewa jirgin samfurin ATR-42 ne, wanda ke kan wata tafiya ta yau da kullum daga Benin zuwa Legas lokacin da hatsarin ya afku, an ce mutane 32 ne ke cikin jirgin, da suka haɗa da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai.
