Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwankwaso Ya Kaddamar Da Kwamitin Yakin Neman Zabensa Na Shugaban Kasa.

Kwankwaso Ya Kaddamar Da Kwamitin Yakin Neman Zabensa Na Shugaban Kasa.

Date:

Jam’iyyar NNPP ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben dan takararta na shugaban kasa, domin samun nasara a zaben 2023.

 

Da yake kaddamar da kwamitin a Abuja, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce dukkan bangarorin za su yi aiki tare domin samun nasarar jam’iyyar NNPP a zaben shugaban kasa na 2023.

 

Ya ce jam’iyyar ta ziyarci dukkan jihohin kasar nan in ban da jihohi uku kuma a duk wuraren da suka ziyarta, jam’iyyar ta ziyarci shugabannin gargajiya da na addini don neman yardarsu.

 

Ya kuma bukaci dukkan yan Najeriya, musamman yan jam’iyyar NNPP, kungiyoyi irin su Kwankwasiyya da TNM da sauransu kan su hada kai don neman goyan bayan al’umma da kuri’unsu.

Latest stories

Related stories